--Advertisement--
Advertisement

BINCIKEN GASKIYA: Bidiyon ana zanga-zanga a fadar sarkin Ilori tsoho ne

Ranar Asabar, wani bidiyon masu zanga-zanga a fadar sarkin Ilori a jihar Kwara na ta yawo a shafukan sada zumunta.

A bidiyon, masu zanga-zangan wadanda yawancin su matasa ne, ana iya jinsu suna ihu a Yarbaci suna cewa “Ebin palu (akwai yunwa a gari)”.

Bidiyon nan da nan ya yadu a shafukan sada zuwunta inda ake ta yada shi ana cewa zanga-zangar ranar asabar aka yi saboda hali na yunwa da ake ciki a kasar.

Najeriya na fuskantar rashin tsaro, karyewar naira da kuma hauhawan kayan masarufi.

Advertisement

Hakan ya janyo zanga-zanga a wasu wurare a kasar nan.

A ranar 5 na watan Febrairu, wadansu a Minna, babban birnin jihar Niger, suka tare hanya don yin zanga-zanga saboda halin tsadar rayuwa a kasar.

Bayan wasu kwanaki, mazauna karamar hukuma Suleja na jihar suma sunyi zanga-zanga saboda tsadar rayuwa.

Advertisement

Hakama a ranar 10 na Febrairu, Wadansu mata ‘yan kasuwa a jihar Legas sunyi zanga-zanga saboda tsadar rayuwa a kasar.

KWANAN NAN AKA YI zanga-zangar?

TheCable, bayan yin bincike ta gano cewa bidiyo iri daya ne ake ta yada wa a kan zanga-zangar.

Wani mai shafi a X mai suna @omoelerinjare, daya tura bidiyon a shafin sa, sama da mutane 360,000 sun gani sannan mutane sama da 2,000 sun kara tura shi.

Advertisement

Advertisement

Binciken da TheCable tayi ya nuna bidiyon tun a 2021 yake yawo a shafukan sada zumunta.

Shima, Ibrahim Sulu-Gambari, sarkin Ilori, a wata sanarwa da ya fitar, yayi watsi da maganar cewa kwanan nan akayi bidiyon da kuma saboda tsadar rayuwa aka yi.

Sarkin yace bidiyon an dauke shi ne tun a 2019, lokacin da zaben 2019 ya gabato.

HUKUNCI

Bidiyon ana zanga-zanga a fadar Sarkin Ilori tsoho ne.

Add a comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

error: Content is protected from copying.