An alakanta wani bidiyo da ke nuna gine-gine suna rushewa da girgizan kasa a garin Taiwan.
A bidiyon, a na iya ganin manyan gine-gine suna rushewa, inda kura ke tashi kuma mazaunan wurin suna ihu.
A saka bidiyon mai tsawon dakika 13 a kafar sada zumunta na X inda mutane sama da 55,000 suka gani.
“Gine-gine da yawa sun rushe sanadiyar girgizan kasa,” inji @patrickhsu0906, wani mai shafi a X.
Advertisement
Mutane da yawa sun yada bidiyon a X tare da cewa a garin Taiwan ne a ka yi girgizan kasa.
“Taipei, Taiwan, an yi girgizan kasa ranar laraba a gabashin garin da safe, mutane 9 sun mutu sannan akalla 963 sun samu rauni, a cewar masu kashe wuta a Taiwan,” inji @ZubairSpanish, wani mai shafi a X.
GIRGIZAN KASA DA AKAYI A TAIWAN
Advertisement
A ranar Laraba, anyi girgizan kasa mai karfi a garin Taiwan, inda gine-gine suka rushe, mutane tara suka mutu sannan sama da 1,000 sun samu rauni.
Duk da aukuwan girgizan kasa ba sabon abu bane a Taiwan, masana sunce wanda a ka yi a ranar laraba ne yafi kowanne karfi da a ka taba yi a cikin shekaru 25.
A 1999, girgizan kasa ya kashe mutane 2,400, kuma mutane 100,000 sun samu rauni sannan gine-gine sama da dubu sun ruguje.
TABBATARWA
Advertisement
TheCable tayi bincike a kan bidiyon inda aka gano bidiyon tun a 27 na Agustan 2021 a ka daura shi a shafin The paper Yunan information platform – wata kafar yada labarai a kasar Sin.
A cewar kafar yada labaran, an rusa wasu manyan gine-gine guda 15 ne a Kunming, a garin Yunnan dake kasar Sin.
An rusa manyan gine-ginen ne saboda sun saba ma wasu ka’idoji na gini sannan an dauka lokaci mai tsawo ana gina su.
An daura bidiyon a ranar 31 na Agustan 2021 a wani shafi a YouTube mai suna USA TODAY.
Advertisement
HUKUNCI
Bidiyon rushewan manyan gine-gine ba shi da alaka da girgizan kasa da a ka yi a Taiwan.
Advertisement
Add a comment