--Advertisement--
Advertisement

BINCIKEN GASKIYA: Kudin tikiti na cinema a Najeriya ne mafi tsada a duniya?

Wani dan kasuwa dake Abuja yace kudin tikiti na cinema a Najeriya ne mafi tsada a duniya.

Dan kasuwan, Yinka Ade-Aluko, shine shugaban Doodle-Film hub.

Ade-Aluko yace sashin cinema a Najeriya masu kudi kawai yake amfanarwa.

Mai shirya fina-finan yace wani bincike da kamfanin sa yayi ne ya gano cewa kudin tikitin cinema a Najeriya “ne yafi na ko ina tsada a duniya” saboda “tsadar shi” kuma marasa hali “basu da kudin” da zasu je suyi kallo.

Advertisement

Saidai, bai bayyana sanda aka yi binciken ba.

Ya gaskiyan maganganun mai shirya fina-finan suke?

ME KE SA A YANKE KUDIN TIKITI NA CINEMA

Advertisement

Kudin tiki na kunshe ne da yawan mutanen da ke zuwa cinema, yanda mutane ke siyan tikiti, haraji, da kuma irin abincin da ake raba ma masu kallo.

Wadansu gidajen cinema irin su IMAX, wanda gidan cinema ne da ke haska fina-finai a babban abun kallo. Hakan kuma ya banbanta su da sauran gidajen cinema na gargajiya.

Gidajen cinema da dama suna barin kwastamomi su siya tikiti ta yanar gizo ko daga wayoyin su.

Duk da cewa ya danganta daga irin dokokin da aka gindaya, wadansu tikiti na cinema na zuwa ne tare da kudin haraji da mai kallo ze biya a lokacin siyan tikiti.

Advertisement

Wadansu gidajen cinema suna ba ma masu kallo ragin kudin tikiti saboda su samu mutane da yawa suzo suyi kallo.

Wadansu kuma suna bada daman a zaba kujeran da za a zauna a cikin cinema din, bada abinci inda duk za a chaji duka abubuwan a kudin tikitin da mai kallo zai biya.

KUDIN TIKITI A KASASHEN DUNIYA

Kudin tikiti na fim iri daya yana ban-banta a kasashen duniya.

Advertisement

Gidajen cinema dake cikin manyan garuruwan kasashe tikitin sun zasu fi tsada saboda yawa mutanen da zasu rika zuwa.

Kudin kama haya, biyan maaikata, da na kulawa da wurin duk suna hade ne a cikin kudin tikitin.

Advertisement

Lokacin da za a haska fim a cikin cinema da kuma na’urorin da za ayi amfani da suma suna daga cikin abubuwan da ke sa tikiti yayi tsada.

A fadin duniya, sana’ar cinema da na hada fina-finai sun ban-banta duk da de ‘yan kasuwa suna zuwa jari don su samu riba.

Advertisement

Misali, fim din da Jason Statham yayi a 2024 mai suna ‘The Bee Keeper’ zai kai $10 a cinema idan za a kalla a garin California, a Amurka sannan kudin zai ragu zuwa $4 a cineman IMAX daki Lekki a jihar Legas.

Kasashe da keda yawan mutane masu zuwa kallo a cinema “suna da daman” sanya kudin tikitin su kar yayi tsada a wasu fina-finai, saboda zasu maida kudin su har suyi riba saboda yawan mutanen da zasu shiga yin kallo.

Advertisement

LEKAWA CIKIN HARKAR CINEMA A NAJERIYA

Manyan gidajen cinema a Najeriya sun hada da Silverbird, Lighthouse, Ozone, Filmhouse, da Genesis.

A Najeriya, zuwa kallan mawaka suyi taro kai tsaye ya riga yin tasiri kafin gidajen cinema na zamani.

Silverbird Group na kamfanin farko da ya fara bude cinema na zamani a Najeriya, inda suka fara a Victoria Island dake Legas a 2004.

Da farko, fina-finai na turawa suka fara, inda daga baya harda fina-finai da aka yi a Najeriya suka fara haskawa.

A tsakiyar 2010, harkar sanya fina-finai DVD ana saidawa.

“Zaka iya kashe naira miliyan 20 a wurin hada fim, a buga a DVD, sai daga karshe ko riban naira miliyan 5 ba za kayi ba saboda masu saida fim din bogi wa masu kallo,” inji wani mai cinema Allen Onyige. “A lokacin da cinema ya fara karbuwa, a 2016 ne.

Netflix ya shigo Afurka a 2016 inda bayan shakara hudu aka dawo daraja kallan fim kai tsaye a yanar gizo.

Harkar cinema a Najeriya yana fuskantar kalubale iri-iri. Kallo kai tsaye a yanar gizo yafi arha wa masu kallo fiye da cinema.

Bayanai daga Inside Nollywood ya nuna a shekara ga adadin mutanen dake zuwa cinema a Najeriya. A 2015 mutane miliyan 2.45 ne. A 2018 ya haura zuwa miliyan 5.43. A 2019 an samu raguwa sannan a 2020 da annoba tazo aka fara karfafa kallo kai tsaye a yanar gizo.

Gidajen cinema a Najeriya har yanzu suna kokarin farfado da kasuwancin su.

A Najeriya, a da, masu hada fina-finai nada wata yarjejeniya na duk ribar da aka samu, masu mai cinema zai dauka kashi 40 da wanda ya hada fim sannan sauran kashi 20 din zai je wurin biyan tallace-tallacen da akayi wa fim din, wanda yawanci haka masu cinema ne keyi.

Yarjejeniyar kashi 60 da na 40 wani lokaci yana nufin masu hada fina-finai baza samu damar maida kudin da suka kashe ba wurin hada fim din.

Sakamakon hakan, wadansu gidajen cinema suka fara hada fina-finai.

Hauhawan farashin kaya, wanda a yanzu yana kashi 29.9, ya kara dumulmiya harkar cinema inda kudin man diesel ya tashi da kuma kudin abubuwa irin su guguru ya tashi.

SHIN, TIKITIN CINEMA NA NAJERIYA NE MAFI TSADA?

TheCable ta tuntubi Yinka Ade-Aluko don jin abubuwan da akayi amfani da wurin gudanar da binciken da kamfanin sa yayi, amma dan kasuwan yace saboda ‘sirrin’ kasuwanci ba zai fada ba.

“Idan zaku duba kudin mafi karancin albashi da kudin tikiti da yawan mutanen da ke zuwa yin kallo a Nollywood, Hollywood, da Bollywood, zai baka mamaki,” dan kasuwan ya fada haka daga baya.

Ade-Aluko a lissafin sa, misali, mai albashin 30,000 zai kashe $18 a kan N1665/$) sannan tikitin fim a Silverbird da ake saidawa a kan N8000 (kusan $4.8) na nufin mai zuwa kallo zai kashe kashi 26.7 na albashin sa a kan fim da bai wuce awa biyu da da kuma guguru.

TheCable ta duba biciken kasuwanci a kan kudin tikiti da aka yi a 2021 na kudin tikitin kasashe 20 a nahiya shida.

A binciken anyi amfani da mafi karancin albashi don tabbatar ko tikitin Najeriya na cikin mafi tsada.

Kasar Venezuela, inda mafi karancin albashin su da kadan ya haura $4 ne daya daga cikin mafi tsada inda tikitin cinema zai mamaye kashi 74 na albashin maaikaci.

TheCable ta duba kudin tikitin cinema a Najeriya tsakanin 2018 zuwa 2024.

A 2018 an saida tikiti a kan N1138 inda a Janairun 2024 aka saida a kan N2571 (an samu karin $1.54 a kan ko wane tikiti.

Tikitin fina-finai da sukafi tsada a cikin binciken sun hada da ‘A Tribe Called Judah’ a kan N3920, ‘Malaika, a kan N3670, da ‘Aquaman: The lost Kingdom’ a kan N4020 ($2.4 a kan N1665/$) – duk a 2024.

TANTANCE KUDIN TIKITI

Ope Ajayi, tsohon janar-manaja na Genesis cinema bai amince da maganan ba da aka tuntube shi ya yi magana a kan ko gaskiya ne kudin tikitin Najeriya ne mafi tsada a duniya.

“Ina mamaki idan an gudanar da binciken yanda ya kamata ko kuma ya na nema suna ne, ” inji shi.

Lebanon ce mai tikitin cinema mafi tsada inda tikiti na mamaye kashi 8.64 na kudin kasar da ake hadawa a wata. Cambodia na biye da ita da kashi 7.85. Sai Mali ne na daya a Afurka mai kashi 6.45 da kuma Kenya a kashi 4.71.

Najeriya ne na biyar da kashi 3.37. Hakan na nufin ba Najeriya bane keda tikiti mafi tsada ba.

ADADIN MUTANEN DA KE ZUWA KALLO

A cikin maganganun Yinka Ade-Aluka, TheCable ta binciki yawan mutanen da ke zuwa kallo a cinema a Najeriya.

An samu bayanai da ke nuna yawan mutanen da suka je yin kallo a cinema daga 2015 zuwa 2023.

Yakuma yi dai-dai da alkaluman da aka samu a Statista.

Bayanan sun nuna a 2023, kashi 1.16 cikin mutane miliyan 226 a Najeriya ne suka yi kallo a cinema.

A 2022, an saida tikitin fina-finai miliyan 981 a India. Idan aka hada shi da yawan yan kasar a shekarar 2019 da mutane sunkai kusan biliyan daya da miliyan dari hudu, zai zama kashi 69.22 ne sukayi kallo a cinema.

A Najeriya ba a taba zuwa kusa da wannan alkaluman ba dukda Nollywood ne na biyu a fannin buga fina-finai.

HUKUNCI

Ta amfani da mafi karancin albashi don a lissafa tsadar kudin tikiti, Najeriya ce ta biyar a cikin kasashe 20 a mafi tsadar tikitin cinema.

Kowace gidan cinema a duka kasashe na da banbancin yanda yake gudanar da kasuwanci.

Duka amsoshin da aka samu iri daya. Ba dai-dai bane cewa Najeriya ne mai tikiti na cinema mafi tsada a duniya.

Add a comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

error: Content is protected from copying.