--Advertisement--

Binciken Gaskiya: Saba ma doka ne idan NNPC ya tura kudin mai zuwa CBN – kamar yadda Atiku yace?

Atiku Abubakar Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yace umarnin da gwamnatin tarayya ta ba kamfanin NNPC na tura kudin da aka samu daga saida mai zuwa babban bankin Najeriya (CBN) ya saba ma doka.

Atiku yayi wannan maganan ne bayan Olayemi Cardoso, gwamnan CBN, ya ce bankin na aiki tare da NNPC don tabbatar da “duka kudin kasar waje da ta samu sun koma hannun CBN”.

Atiku yace maganar gwamnan CBN ya nuna ana yi ma NNPC kutse a aikin su.

“Babu kyakyyawan nufi a umarnin da aka bayar na CBN ta na karban kudin mai daga NNPCL. Dole ne a fada cewa wannan abun ya saba ma doka,” inji Atiku.

Advertisement

“Wannan umarnin kutse ne a cikin aikin NNPCL.”

Atiku yayi kira ga gwamnati da “ta girmama dokokin kasa ta bar NNPCL yayi aikin sa a matsayin kamfani mai zaman kansa”.

TABBATARWA

Advertisement

A watan Yulin 2022, kamfanin ya zama mai zaman kansa.

Dayake magana a taron zamar da kamfanin mai zaman kansa, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yace NNPCL zai yi aiki “ba tare da kutse daga gwamnati ba”.

Saidai, gwamnatin tarayya mai hannun jari mafi yawa a kamfanin – duk da kamfanin nada shirin saida ma ‘yan kasuwa da hannun jari a nan gaba.

ME DOKA YA CE?

Advertisement

NNPC zata ajiye kashi 20 na ribar da ta samu inda kuma zata tura ma gwamnatin tarayya kashi 80 a matsayin ta na mai hannun jari.

ME MASANA SUKA CE?

Da yake magana a kan lamarin, Oyeyemi Oke, wani lauya a AO2LAW, yace NNPC kamfani ne mai zaman kansa.

A wani taro da ranar 8 na Febrairun 2024 a Abuja, NNPC da CBN sun sanar da cewa “sun sake duba yiwuwar NNPCL ya ajiye wani daga cikin kudin kamfanin a hannun CBN”.

Advertisement

A wata sanarwa da suka fitar, CBN da NNPC sunce ajiyan kudin ba zai hana NNPC yin hulda da sauran bankuna ba.

Shima da yake magana a kan batun, Jide Prat, wani kwararre a fannin mai da gas, yace ba saba ma doka bane yin hakan. Yace duk da cewa NNPC kamfani ne mai zaman kansa, mallakin gwamnatin tarayya ne.

Advertisement

A Disamban 2023, Mele Kyari, shugaban NNPC, yace kamfanin ya tura tiriliyan 4.5 a asusun gwamnatin tarayya daga Janairu zuwa Oktoba na 2023.

HUKUNCI

Advertisement

Maganar Atiku cewa saba ma doka ne idan NNPC ta tura kudin saida mai zuwa CBN ba dai-dai bane.

Gwamnati itace tafi hannun jari a kamfanin sannan ita keda kashi 80 na duk ribar da kamfanin ta samu.

Advertisement
Add a comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

error: Content is protected from copying.