Labarai da dama a shafukan sada zumunta na cewa shan ruwan kubewa na sa mace ta dauka ciki da wuri.
Ruwan kubewa a cewan wadannan labaran, na nufin kubewa da aka yanka kanana aka jika a ruwa.
Bayan amfanin da akeyi da kubewa a yin abinci, qadansu na cewa a na iya amfani da shi domin a saurin daukan ciki.
A wani bidiyo da aka daura a Facebook, wata mata mai dauke da juna biyu ta nuna yanda tayi hadin ruwan kubewan ta domin “haihuwa cikin sauki” da kuma “haihuwa ba tare da anyi aiki ba”.
Advertisement
A bidiyon, matar ta yanka kubewa kanana ta jefa a cikin robobi na ruwa sannan ta rufe kuma ta bada shawaran a adana a firij na awa 24, inda daganan ta tsiyaye ruwan sannan ta kara wadansu ‘yayan itatuwa domin kara masa armashi.
Bidiyon mutane 944 sun gani, mutane 59 sun danna alaman so sannan mutane tara sunyi sharhi akai inda kuma aka tura shi zuwa wani shafi da keda sama mutane 427,000 a ciki.
DAUKAN CIKI
Advertisement
Mace na daukan ciki ne idan kwai na hallita da ke cikin jikin ta ya hadu da maniyyin namiji.
A yayin da mace ke dauke da juna biyu, likitoci sun bada shawarar ta yawaita sha da cin abubuwa masu gina jiki.
TABBATAR DA MAGANAR SHAN RUWAN KUBEWA
TheCable ta tattauna da Elizabeth Kembe, wata farfesa a jami’ar Benue. Kembe tace kubewa abinci ne mai dauke kayan gina jiki, amma dai, babu tabbacin yana saka saurin daukan ciki ko saukaka haihuwa.
Advertisement
Wani bincike da akayi a Amurka ya nuna ya na da amfani a na cin kubewa. Binciken yace kubewa na taimaka ma mutane masu fama da ciwon suga.
Da ya tattaunawa da TheCable, Mohammed Bukar, wani farfesa a jami’ar Maiduguri da ke jihar Borno, yace babu wani da zai iya tabbatar da maganar domin ba a gudanar da bincike a kai ba.
HUKUNCI
Maganar cewa kubewa na saka mace tayi saurin daukan ciki da kuma saukaka haihuwa ba gaskiya bane domin babu wani bincike ja kimiyya da ya tabbatar da hakan.
Advertisement
Add a comment