Labarin cewa Yahaya Bello, tsohon gwamnan jihar Kogi, ya halarci taron da Shuganam kasa Bola Tinubu yayi da gwamnoni da wasu ministoci a fadar sa dake Abuje a ranar alhamis.
A taron, Tinubu da gwamnonin sun amince da bukatar karin daukan ‘yan sanda domin magance matsalar tsaro dake yaduwa a kasar.
Bayan taron, wani mai shafi a X ya tura hoton Bello a tsaye tare da sauran gwamnoni da Tinubu a fadar shugaban kasa.
“Yahaya Bello har yanzu ya na halartar zaman kwamitin zartarwa a matsayin gwamnan jihar Kogi duk da ya mika ma wani mulki,” inji rubutun.
Advertisement
Wadansu a shafin su na X suma sunce Bello ya halarci taron da Tinubu yayi da gwamnoni duk da ya mika mulki a watan Janairu.
A hoton dake yawo, ana iya ganin Yahaya Bello a tsaye a gefen Hope Uzodinma, gwamnan Imo da Babajide Sanwo-Olu, gwamnan Legas da kuma Tinubu a tsaye a tsakiyan sauran gwamnoni sun zagaye shi.
Saidai, Yahaya Bello ya halarci taron?
Advertisement
Bello ne gwamnan jigar Kogi a karkashin jam’iyar All Progressives Congress (APC) daga 2016 zuwa 2024. Usman Ododo ne ya karba mulki daga Bello wanda aka rantsar a ranar 27 na Janairu.
A matsayin shi na tsohon gwamna, Bello ba shi da damar halartar taron gwamnoni da shugaban kasa; Ododo ne ko kuma mataimakin sa ne kawai zasu iya.
Binciken TheCable ya nuna hoton dake yawo, shafin fadar shugaban kasa na X ne suka fara tura hoton. Anyi amfani da hoton ne don yin bayanin abubuwan da aka tattauna a taron.
Karin bincike ya nuna an dauka hoton ne a taron farko da Tinubi yayi da gwamnoni bayan ya zama shugaban kasa. Bello a lokacin shine gwamnan jihar Kogi.
Advertisement
Hoton tun watan Yuni ma 2023 aka dauke shi.
Sannan, kayan da shuagabannin suka saka a taron da suka yi bara ya banbanta da na taron da aka yi ranar alhamis.
Fadar shugaban kasa tuni ta chanza tsohon hoton da ta saka a shafin ta da hotunan da aka yi a ranar alhamis.
Ododo ya halarci taron kuma an dauke shi hotuna.
Advertisement
HUKUNCI
Duk da shafin fadar shugaban kasa na X ne suka fara tura hoton, maganar cewa Bello ya halarci taron gwamnoni da Tinubu a fadar shugabn kasa ranar alhamis ba gaskiya bane.
Advertisement
Ga ainihin hotunan da aka dauka a taron.
Advertisement
Add a comment