--Advertisement--
Advertisement

Kwankwaso ya ciyo bashi – Kudin da ake bin Kano ya karu sama da 1000% tsakanin 2011 da 2015

Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takaran shugaban kasa a jam’iyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), yace a shekaru takwas dinsa na mulki a Kano, gwamnatin sa bata taba cin bashi ba.

Kwankwaso yayi wannan maganan ne a ranar Asabar, 19 Nuwamba a wurin taro na yan takaran shugaban kasa mai taken ‘The Candidates’, wanda Kadaria Ahmed, wsta yar jarida ce ta jagoranci taron.

Rabiu Kwankwaso bai ara ko da naira daya daga wurin banki ba, ko hannun wani dake kasar nan ko a kasar waje,” inji shi.

“Ina daga cikin gwamnonin da basu taba cin bashi ba, kuma ma, na tsani cin bashi. Bama haka ba, a 1999, sanda na zama gwamna, na gaji bashi dayawa wanda kuma duk na biya a tsakanin shekaru hudu.

Advertisement

“Na fadi a zaben 2003. Bayan shekara takwas, na dawo kuma na tarar da wani bashin kuma na biya a cikin shekara hudu. Nabar Kano ba tare da bashin ko naira daya ba.”

Ya kara yin wannan maganan a ranar Lahadi, Nuwamba 13 sanda ya halarci taron yan takaran shugaban kasa da Channels Television suka shirya.

Dayake amsa yadda zai samo kudi da zaiyi aiki da ba tare da ciyo bashi ba bayan yayi kasafin kudi idan ya zama shugaban kasa, Kwankwaso yace dayake gwamna a Kano, bai taba cin bashi ba.

Advertisement

“A Kano, bamu taba samun matsalan kasafin kudi mai tangarda ba saboda muna sanya ido akan abubuwan dake zuwa kuma muna duba abubuwan da sukafi muhimmanci da yakamata ayi. Bana cikin wadanda suke gaggawan ciyo bashi domin suyi wani abu,” inji shi.

“Akwai kudi mai wadata a kasar nan. Duk wanda yace babu kudi a kasar nan toh koh bai sani bane kokuma so yake ya yaudari mutane. Akwai isasshe da zai kula da kowa da kowa a kasar nan.

“Munyi a da a Kano daga 1999 zuwa 2003. Mun tarar da bashi dayawa kuma mun biya duka. Bayan shekara takwas dana kara zama gwamna, na samu bashi na miliyoyin daloli wanda kuma muka biya kafun nasauka a 2015.

“Ina maganan cin bashin kudi daga banki ko hannun wani. Bamu taba ansan bashi ba na tsawon shekaru takwas da nake gwamna.”

Advertisement

A 2021, a wani hira da Arise TV, Kwankwaso ya zargi Abdullahi Ganduje da jefa Kano cikin tarin bashi. Yakara da cewa, a cikin shekaru takwas da yayi mulki a Kano, bai taba cin bashi ba ko na naira daya.

Ya gaskiyan maganan cewa Kano bata taba cin bashi ba sanda Kwankwaso ke gwamna?

Rabiu Kwankwaso, shine gwamnan jihar Kano tsakanin 1999 da 2003 

Ya fadi zaben sa na neman yin tazarce a 2003. Biyo bayan hakan, aka nada shi ministan tsaro daga 2003-2007.

Advertisement

A 2011, aka zabe shi ya kara zama gwamna a jihar Kano.

Ofishin kula da bashi (DMO) basu da bayanai a shafin su da ya goyi bayan maganan cewa Kwankwaso ya ciyo ko bai ciyo bashi ba a lokacin mulkinsa nafarko ba a tsakanin 1999 da 2003.

Advertisement

Bashin waje ya ragu da 9.89% tsakanin 2011 da 2015

A cewar bayanai daga DMO, a 2011, Kano nada bashin waje na $63.94 miliyan da Kwankwaso ya hau mulki a wa’adin sa na biyu.

Advertisement

A lokacin da ya sauka daga mulki, yawan bashin ya ragu zuwa $57.61 miliyan, inda aka samu ragin 9.89%.

Advertisement

Bashin cikin gida ya karu sama da 1000%.

Bayanai daga DMO sun nuna cewa tsakanin 2011 da 2015, lokacin da Kwankwaso yayi mulkinsa ba biyu, bashin cikin gida na Kano ya karu da  1008%.

A 2011 da aka sake zaben sa gwamna, akwai bashin cikin gida na N5.87 biliyan a kasa. A 2015, daya bar ofis, bashin da ake bin jihar ya karu zuwa N65 biliyan, karin 1008%.

A zahiri, karin yawan bashin cikin gida ba lallai daga yawan aran kudi bane idan akwai abubuwa da suka shafi karin hauhawan farashin chanji a kudaden kasashen waje.

Binciken TheCable ya nuna cewa farashin chanjin kudi bashi bane ya janyo karin yawan bashin da ake bin jihar Kano. Kuma kari a  yawan intrest a tsakanin shekara 4 bazai sa bashin da ake bin jihar ya haura da kashi 1008.

A lokacin ma, farshin da ake chanza dollar zuwa naira yana kan N155 duk $1 a 2011, da kuma N197 duk $1 a 2015.

Abdullahi Ganduje ya shaida cewa jihar ta ranci kudi.

Kafun su samu matsala su bata, Ganduje, mataimakin Kwankwaso, wanda ya gaji mulkin a 2015, yace ba wani abu bane dan wanda yayi mulki kafun shi yabar jihar da bashin sama da naira biliyan 300 – yawan kudin da ma ya wuce yadda DMO ya fada.

“Bana tunanin Kwankwaso yayi laifi saboda yabar bashi dayawa a jihar saboda duk tsare-tsaren da akayi, tare dani akayi,” inji Ganduje.

Ya kuma yi Allah wadai da masu sukar Kwankwaso saboda ya tara bashi a jihar, ya kara da cewa ragewan farashin mai ne ya janyo yawan kudin dake shigowa ya rage.

Ya kuma ce Kwankwaso na bukatar a yaba masa akan ayyukan da yayi a jihar duk da nauyi bashin da ke kanta.

“Nasan komai daya faru, abubuwan da muke tsammani nada yawa kuma mun zata abubuwa zasu ci gaba da tafiya lafia sai kwatsam kawai raguwar farashin mai yazo,” a cewar Ganduje a wani rahoto a 2015.

“Sabods haka, barin bashi ma wata gwamnati ta gada ba wani abu bane. Duk masu sukar yin hakan suma zasuyi hakan ko suyi fiye dashi lokacin da suka karba ragamar mulki. Gwamnan mu, Kwankwaso, yana bukatar ya jinjina masa ne a bisa aiki da gyara da yayi a jihar Kano.”

A cewar wani rahoton 2015, ‘yan Kwangila na cikin gida sun bukaci hukumomin yakar rashawa dasu gudanar da bincike akan Kwankwaso saboda zargin da ake masa na tara bashin naira biliyan 200 da kuma karya kananan yan kasuwa kafun ya gudu zuwa majalisar dattijai.

A 2015, Auduwa Maitangaran, shugaban yan Kwangilan cikin gida na Nijeriya, yace sama da yan kwangila 50 aka tura gidan yari da kuma sama da 100 aka kwantar da a asibiti saboda rashin biyan su kudin su da gwamnatin Kwankwaso takiyi.

Mun rasa yan kungiya sama da 40 da suka rasu sanadiyar rashin lafia da sukayi sakamakon daukan lokacin da akayi wurin biyan su kudin su da waccan gwamnatin data gabata tayi,” inji shi.

Dan kwangilan yace “Kwankwaso ya biya 30% ne kawai a ayyukan da yayi a tsawon shekaru hudu”, yabar 70% ba a biya ba, ya kara da cewa 50% na yan kwangila ba a biya su kudin su ba har da gwamnatin tazo karshe.

“Alhaji Idi Bilya, wani dan kungiyar mu, ya rasu ne saboda hawan jini sakamakon rashin biyan sa kudin sa da ba ayi ba da kuma wani Alhaji Ibrahim Carpenter da yake da naira miliyan 50 a hannun gwamnatin jihar Kano bazai iya fito maka da naira 5,000 a yanzu ba. Wannan zalunci ne,” a cewar shugaban yan kwangila a rahoton 2015.

Muhammad Garba, wani tsohon kwamishina na labarai, ya zargi Kwankwaso da karban bashin naira biliyan 4.1 na yan fensho domin ya gina gidajen ma’aikata.

Daily Trust ta rawaito cewa Garba yace: “Kwankwaso ya ara kudi har naira biliyan 4.1 na yan fansho domin gina Bandirawo da Amana Housing Estates da manufar yan fansho su amfana daga gidajen.

“Amma daya gane cewa gidajen sunyi tsada da yawa ma yan fansho din su iya kama gidajen, sai ya soke 50% na farashin gidajen, kuma duk da haka, yan fanshon sun kasa siyan gidan.”

Hukunci

Maganar Kwankwaso cewa gwamnatinsa bata taba cin bashi ba dayake gwamnan Kano ba gaskiya bane. Bayanai sun nuna cewa bashin da ake bin Kano ya haura da 1008%. Kuma, wanda ya anshi mulki daga hannunshi da kuma yan kwangila a jihar sun bayyana cewa bashin cikin gida na jihar ya karu saboda bashi da akaci.

Add a comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

error: Content is protected from copying.