Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra, kuma dan takaran shugaban kasa na jam’iyar Labour (LP) yayi maganganu da dama yayin da yake bayyana tsare-tsaren sa na tattalin arzikinsa a wurin taron tattaunawa na ‘yan takarar shugaban kasa da Nigerian Economic Summit Group (NESG) suka shirya.
TheCable ta bincika wasu daga cikin maganganun dayayi, kuma ga abun da muka samo.
Da’awar daya: “Bangaren hada abubuwa na bada gudun mawan kasa da kashi 10 cikin 100 ma GDP”.
Hukunci: Gaskiya
Advertisement
A cewar cibiyar kiddidiga ta kasa (NBS), rahoton kashi na uku a 2022 ya nuna cewa bangaren hada abubawa ya bada gudun mawan kashi 8.59 cikin 100 ma GDP.
Alkaluman yayi kasa da kashi 8.96 cikin 100 da aka samu a kashi na uku a 2021, da kuma kashi 8.65 cikin 100 a kashi na biyu na 2022.
Da’awar biyu: “Bangaren noma na bada gudun mawan kusan kashi 26 ma GDP na Nijeriya”.
Advertisement
Hukunci: Karya
Bangaren noma ya bada gudun mawan kashi 29.67 cikin 100 ma GDP a sashi na uku na 2022, inda ya ragu daga kashi 29.94 cikin 100 da aka samu a kashi na uku na 2021.
A cewar bayanan da NBS ta fitar, bagaren da ba na mai ba ya babada gudun mawan kashi 94.34 cikin 100 ma GDP. Bangaren mai ya bada gudunmawan kashi 5.66 cikin dari kawai, inda ya ragu daga kashi 7.49 a kashi na uku a 2021, da kashi 6.33 cikin 100 a kashi na biyu a 2022.
Da’awar uku: “Rashin aikin yi a Kenya na kasa da kashi 10 cikin 100″.
Advertisement
Hukunci: Gaskiya.
A cewar Statista da Macrotrends, bayanan baya da aka saka a 2021, na cewa rashin aikinyi a Kenya kashi 5.74 ne cikin 100.
Rashin aikin yi yana nufin rabon ma’aikata wanda ba shi da aiki, amma akwai kuma neman aikin yi.
A 2020, yana kashi 5.73 cikin 100, 5.01 cikin 100 a 2019 da kuma 4.25 a 2018.
Advertisement
Tsakanin 2003 da 2016, alkaluman rashin aikinyi a yankin Afurka ta kudu na a lokuta daban-daban kasa da kashi uku cikin 100.
Da’awar hudu: “kasar Netherlands nada girman 33,000 sq km.”
Advertisement
Hukunci: Gaskiya.
Bankin duniya ya saka girman kasar Netherlands a 33,670km sq.
Advertisement
Da’awar biyar: “Kasar Netherlands ta fitar da kayan amfanin noma zuwa kasashen waje na $biliyan 120 a 2021”
Hukunci: Karya
Advertisement
Gabadaya abun da Netherlands ta fidda a 2021 $biliyan 130.7 ne ba $biliyan 120 ba.
A kasar Netherlands, an kasa bangaren fitar da amfanin gona zuwa kashi biyu.
Abubuwan da ke da alaƙa da aikin noma suna nufin samfuran da ba za a iya ci ba waɗanda ake samarwa don fannin aikin gona a gida ko waje, yayin da fitar da noma kai tsaye yana nufin samfuran da ake samarwa – sarrafa ko ba a sarrafa su – a cikin Netherlands.
A cewar alkaluman 2021, gaba daya abun da aka fitar zuwa kasashen waje na amfanin gona €biliyan 122 ne ($biliyan 130.7). Kayan da aka fidda yakai kusan €biliyan 106, yayin da wanda ba fitar zuwa kasashen waje ba ya tsaya a €biliyan 16.
Da’awar shida: “Na san cewa babbar kasa, wadda ita ce Amurka a yau tana da kusan kashi 90 cikin 100 na bashin GDP, na biyu China tana da sama da kashi 60 cikin 100 na GDP, Japan tana da kashi 230. Hatta Singapore da muke ambata a kowace rana bashin kashi 130 ne ga GDP. Matsalar da muke da ita a matsayinmu na kasa ita ce kudaden da muke karba suna bacewa”.
Hukunci: Karya.
Ko da yake binciken da TheCable ta yi ya nuna cewa kasashen hudu da aka ambata duk suna da basussuka, alkaluman da dan takaran shugaban kasan ya ambata duk ba daidai bane.
Investopedia ta ayyana bashi-zuwa-GDP a matsayin rabon da ya kwatanta bashin jama’a na kasa da babban kayan cikin gida (GDP). Ana samun wannan rabo ne ta hanyar kwatanta abin da kasa take bin kasa da abin da take nomawa. Hakanan yana iya bayyana adadin shekarun da ake buƙata don biyan bashi idan GDP na ƙasa ya keɓe ga hakan kawai.
Amurka
Adadin bashi-zuwa-GDP a Amurka kamar na 2022 shine kashi 124, ba kashi 90 cikin dari ba kamar yadda Obi ya yi iƙirari.
A cewar bayanan fiscal data, wani shafi dake yin bayani akan bangaren kudaden Amurka, bashin Amurka a hade da GDP yana kashi 124 cikin 100 a cewar bayanan 2022.
A cikin 2013, Amurka ta zarce kashi 100 na bashi-zuwa-GDP rabo lokacin da bashi da GDP ya kai kusan dala tiriliyan 16.7.
China
A karshen shekarar 2022, yawan bashin da kasar Sin ta samu zuwa GDP ya kai kashi 76.9 cikin dari, ba kashi 60 cikin dari ba kamar yadda Obi ya bayyana.
Japan
A watan Satumbar 2022, bashin Japan ya kai kashi 263.9 na GDPn sa kuma ba kashi 230 cikin 100 ba bisa bayanin Obi. Alkaluman 2022 kari ne akan kashi 259.4 da aka samu lokacin annobar COVID-19.
Singapore
A cewar International Monetary Fund (IMF) bashin Singapore hade da GDP na kashi 141.1, ba kashi 130 kamar yadda Obi yace.
Da’awar bakwai: “Ana bin Nijeriya bashin naira tiriliyan 77.
Hukunci: Karya. Bashin Najeriya a halin yanzu ya kai Naira tiriliyan 44.06 ba Naira tiriliyan 77 ba.
Ofishin kula da bashi (DMO) a Satumban 2022 sun fitar da rahoto akan yawan bashin da ake bin Nijeriya.
Rahoton ya ce, bashin da ake bin Najeriya, wanda ya kunshi basussukan da gwamnatin jihar ke bin kasar – ciki har da babban birnin tarayya (FCT) – da na gwamnatin tarayya Naira tiriliyan 44.06.
An cimma wannan adadi ne ta hanyar tara basussukan da gwamnatin jihar ke bin jihar – ciki har da yankin babban birnin tarayya (FCT) – da na gwamnatin tarayya.
Basusukan cikin gida na kasar a halin yanzu ya kai Naira tiriliyan 26.92, yayin da bashin waje ya kai Naira tiriliyan 17.14.
Sai dai kuma, Patience Oniha, babban darakta na DMO, in ji shirin gwamnatin tarayya na tabbatar da basussukan – hanyoyi da hanyoyin – daga babban bankin zai fitar da basussukan kasar zuwa kusan Naira tiriliyan 77.
Hakan na nufin gwamnatin da zata zo a gaba za ta gaji bashin kusan naira tiriliyan 77 a lokacin da mulkin shugaba Muhammadu Buhari zai kare a watan Mayu.
Da’awar takwas: “Jimlar fitar da Najeriya zuwa waje a 2021 ya kai N18.9trn.”
Hukunci: Gaskiya.
Bayanan da babban bankin Nijeriya (CBN) ya fitar na cewa a 2021, gaba daya abun kasar ta fidda zuwa kasashen waje $biliyan 46.69 ne, inda aka samu kari daga $biliyan 35.9 da aka samu a shekara da yazo kafun shi.
TheCable ta kuma yi nazari kan bayanan NBS kan cinikin kasashen waje wanda ya nuna cewa an kiyasta kayayyakin da Najeriya ke fitarwa zuwa kasashen waje sun kai Naira tiriliyan 18.9 a shekarar 2021, kwatankwacin dala biliyan 47.3 wanda ya kai matsakaicin kudin canji na N399.6 a shekarar 2021.
Karin rahoto daga Busola Aro
Add a comment